Wasu mata dauke da bamabamai sun tada bam a bayan garin Maiduguri da yammacin ranar Talata.
‘Yan kunar bakin waken sun tada bamabaman ne dake daure a jikin su lokacin da suke gudun wasu ‘yan banga dake sintiri.
A wannan daren ne rundunan ‘yan sandan jihar ta sanar da afkuwar wannan mummunar al’amari inda ta ba da bayanan cewa ‘yan matan su uku ne kuma sun ta da bam din ne a titin Zambia dake kusa da cikin Maiduguri.
‘’Ko da ‘yan banga far musu sai suka tada bam din da suke dauke da shi.’’