Fadar shugaban kasa ta karyata labarin SaharaReporters kan rashin lafiyar Buhari

0

Mai taimakawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan sababbin kafafen yada Labarai Bashir Ahmad ya karyata rahoton gidan jaridar SaharaReporters wai shugaban kasa Muhammadu Buhari baya iya magana da kowa kuma baya iya cin abinci saboda rashin lafiya da ya ke fama dashi a halin yanzu.

Bashir ya sanar da hakanne a shafin sadar da zumuntarsa na Facebook Inda ya ce babu kanshin gaskiya a wannan Labari na SaharaReporters.

” Wannan labari ko kadan ba gaskiya a cikin sa, kamar yadda a makon da ya gabata Garba Shehu ya bayyana babu bukatar tashin hankali game da lafiyar ta Shugaban Kasa.

“Muna da addu’ar Allah ya ci gaba da kula da shi a wannan lokaci da yake ci gaba da samun sauki daga rashin lafiyarsa.”

Share.

game da Author