Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yabawa Sa Gbagyi, Danjuma Barde kan namijin kokarin da yayi wajen kwantar da hankalin mazauna unguwannin Narayi da Sabon-Tasha da ke Kaduna da rikici ya nemi ya tashi a unguwannin.
El-Rufai ya sanar da cewa gwamnati ta kafa kwamiti domin gano dalilin da ya sa hakan ya faru a unguwannin.
Matasa a unguwannin Sabon Tasha da Narayi sun fito dauke da sanduna a titunan unguwannin suna neman tada fitina.
Wasu sun rur-rufe manyan hanyoyi da taya inda suka banka musu wuta.
Jami’an tsaro basu yi kasa- kasa ba wajen tarwatsa matasan sannan kuma an kama wadasu da ga cikin masu shin tada zaune tsaye a unguwannin.
Jami’an ‘yan sanda sun yi kira ga mutane da su dai na yada jita-jita a jihar.
Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan yau a Kaduna.