Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya karawa mai taimaka masa na fannin yada labarai Samuel Aruwan da Maryam Abubakar na fannin sababbin kafafen yada labarai matsayi.
Samuel ya zama babban mai taimakawa gwamna El-Rufai na musamman a fannin yada labarai.
Samuel gogaggen dan jarida ne inda yayi aiki a gidajen jaridun Blueprint da Leadership kafin wannan aiki da yake yi.
Ita ma Maryam Abubakar ta samu irin wannan karin girman inda yanzu ita ce babban mai taimakawa gwamna El-Rufai ta musamman a fannin sababbin kafafen yada labarai.
El- Rufai ya ce yayi haka ne ganin irin kwazon da su keyi musamman wajen ganin sun sanar da wayar da kan mutane manufofin gwamnatin jihar.