Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i JAMB ta ce ba za ta saki sakamakon daliban da ta kama suna satan ansa ba a jarabawar daya gabata.
Shugaban hukumar Ishaq Oloyede ne ya fadi hakan a wata hira da yayi da gidan talabijin din Channels.
Oloyede ya ce hukumar ta yanke shawarar yin hakan ne duk da ta yi alkawarin sakin sakamakon jarabawar awowi 24 bayan an gama jarabawar saboda matsalolin satar ansa da tayi fama dashi.
“ Mun gano cewa wadansu daga cikin daliban da suka rubuta jarabawar sun yi ta satan ansa. Mun gano hakan ne ta na’urar daukar hoto da bidiyo da muka saka a dakunan daukar jarabawar.”
Yace hukumar ta saka irin wadan nan na’u’rori ne saboda ta kama daliban da suke satan ansa a lokacin jarabawar sannan kuma yayi kira ga ‘yan Najeriya da su taimakawa hukumar wajen ganin ta sami nasara akan abinda ta sa a gaba na samun tsaftacaccen jarabawa.