TAMBAYA: Allah ya gafarta malam inayin alwala ne, nakai wajen shafan kunne sai tusa tazo min nayi, shin sai na dawo daga farko kenan na sako?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Lallai mai alwalan da alwalar sa ta war-ware a farkon alwala, ko a tsakiya ko a karshe, kai harma bayan kammala alwalan hukuncinsu daya ne.
Dukkan wanda alwalar sa ta baci, to, zai sake sabuwar alwala ne. Amma idan alwala ta baci a farko, ko tsakiya ko gab da karshe, to, mai alwalan zai sako alwalan sa ne tun daga farko.
Da fatan mai tambaya ya fahimta.
Farillan alwala
Farillan alwala guda 7 ne:
Niyya
Wanke fuska
Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu
Shafar kai
Wanke kafafuwa
Cuccudawa
Gaggautawa
Sunnonin alwala
Wanke hannaye zuwa wuyan hannu
Kuskure baki
Shaka ruwa
Fyacewa
Juyo da shafar kai
Shafar kunnuwa
Sabunta ruwa agaresu
Jeranta tsakanin farillah
Mustahabban alwala
Yin Bismillah
Goga Auwaki
Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye
Farawa daga goshi
Jeranta sunnoni
Karanta ruwa a bisa gabobi
Gabatar da dama kafin hau.