Dalilin da ya sa mu ke binciken Sarkin Kano Muhammadu Sanusi -Kakakin Majalisa

0

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhassan Rirum, ya bayyana cewa binciken da suka fara a kan Mai Martaba Sarkin Kano, ba shi da wata alaka da wancan bincike da hukumar karbar koken jama’a ta gwamnatin jihar ke gudanarwa.

Ya bayyana cewa binciken da majalisar ta fara ya danganci sarkin ne shi kan sa, sakamakon wani kudiri da aka gabatar a majalisa da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Nassarawa, Ibrahim Gama ya gabatar a ranar Laraba.

A ranar Laraba ne dai Gama ya gabatar da caje-cajen laifuka har guda takwas da ya nemi a kafa kwamiti domin a binciki Sarki, wanda kuma a nan take dan majalisa mai wakiltar birni da kewaye, Baffa Babba Dan’Agundi ya goyi baya.

Tuhumomin da ake yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II sun hada laifin bata suna, karya ka’idar aikin ofishin sarki, rashin bin tsarin ka’idar fadar sarki, shiga sha’anin siyasa da na addini.

Sauran tuhume-tuhumen sun hada da furta maganganun da ba su dace ba, kashe kudaden baitulmali ba bisa ka’ida ba, rashin kyakkyawan wakilci a wurin taro da kuma sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Mambobin kwamitin binciken dai sun hada da Abdul Madari na karamar hukumar Ajingi, a matsayin shugaba, sai Baffa Babba Dan Agundi a matsayin mataimakin shugaba. Akwai kuma dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kiru, Kabiru Dachi.

Sauran sun hada da na Dambatta, Sani Maidaji, Abba Garko daga Garko da kuma jami’ai biyu daga sashen kula da shari’a da lauyoyi na majalisar. An dai ba su wa’adin makonni biyu su kammala binciken.

Share.

game da Author