A wani rahoto da dumi-duminsa da ga jihar Cross-Rivers, jami’an rundunar sojin ruwa sun kai farmaki a daren Talatan nan wani ofishin ‘yan sanda dake garin Calabar in da suka yi ta barin wuta ba kakkautawa.
Kamar yadda muka jiyo daga majiyar, Jami’an rundunonin tsaron biyu sun sami sabani ne bayan wani dan sanda ya tsayar da wani jami’in sojin ruwa da ya ki tsaya wa wutan hanya.
Duk da kwamishinan ‘yan sandan jihar da shugaban rundunar sojin ruwa na jihar sun sasanta lamarin, da karfe 8 din daren yau sai ga sojojin sun dawo dauke da makamai su kayi ta barin wuta a ofishin ‘yan sandan.
Wani mazaunin unguwan yace akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu inda har yanzu da muke rubuta wannan labari ofishin ‘yan sandan na nan yana ci da wuta.