Cutar da yake kama Tomatir mai suna ‘Tuta Absoluta’ ya bannata gonakin timatir a wasu kananan hukumomi uku dake jihar Gombe.
Anyi fama da wannan cuta mai suna ‘Tuta Absoluta’ a shekarar bara inda manoman timatir suka yi hasaran amfanin gonarsu masu yawa musamman a garkuwa Arewacin Najeriya.
Wani jami’I a ma’aikatar kula da ayyukan Gona na jihar Gombe, mai suna Gombe ADP Abba Dreba, yace sun sami sanarwan bullowar cutar ‘Tuta Absoluta a kananan hukumomin Akko, Kwami da Yemaltu-Deba.
“ Gabadaya gonakin timatir dake yankunan nan sun lalace sanadiyyar yaduwar wannan cuta.
Yace da zarar cutar ta kama gonar timatir, cikin makonni biyu za ka ga ya lalata ta duk.
Yayi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo wa manoman timatir dauki musamman a wadanna kananan hukumomi da ya ambato.
Babban Darektan ma’aikatar kula da ayyukan gona na jihar Gombe Sunday Lah, ya shawarci manoma da su dan dakata tukuna damina ya kankama kafin su koma gona.
Ya ce yin hakan zai rage hasaran da manoma kan iya fadawa.