Gwamnatin Najeriya ta kara tabbatar wa ‘yan Najeriya shirinta na ganin cewa ta kawar da cutar shan inna a kasar ta hanyar wadatar da jihohin kasa da kudade domin kawo karshen cutar.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da hakan a taron da aka yi don samar da mafita akan hakan.
Osinbajo ya ce cutar shan inna ta sake bullowa ne bayan kasa Najeriya ta yi shekaru uku ba’a sami sanarwan sake bullowar ta ba.
Ya ce hakan ya faru ne saboda aiyukkan kungiyar Boko Haram wanda ya hana ma’aikatan rigakafin cutar shiga wasu garuruwa a yankin.
Osinbajo ya yi kira ga gwamnonin da suka halarci taron musamman gwamnonin yankin Arewa Maso Gabas da su sa himma wajen samar da mafita kan yadda mutanen yankinsu za su kubuta da ga wannan annoba.
Ya kuma ce gwamnatin Najeriya za ta wadata jihohin da duk kudaden da suke bukata domin kawar da cutar gaba daya a kasa Najeriya.
Shugaban kungiyar gwamnonin kasa Najeriya kuma gwamnan jihar Zamfara Abdulazeez Yari da kungiyoyin bada agaji ta duniya sun jinjina wa gwamnatin Najeriya kan kokarin da take yi wajen kawar da cutar daga kasar baki daya.