A kalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar bullowar cutar sankarau a kauyen Tsabu da ke karamar hukumar Mai’adua jihar Katsina.
Shugaban cibiyar kiwon lafiya na karamar hukumar Mai’adua Nasiru Mani ne da yake zantawa da kafanin dillancin labarai a garin Mai’adua ranar Alhamis.
Mani ya ce sun sami labarin bullowar cutar kwanaki biyu da suka wuce inda a tabbatar da mutane 16 sun kamu da cutar wanda a ciki takwas daga cikin su suka rasa rayukansu.
Ya ce sauran mutanen na kwance a asibitocin dake Mai’adua da Daura.
” Bayan mun sami labarin bullowar cutar ne muka aika da ma’aikatan kiwon lafiya domin su taimakawa mutanen garin.”
” Ina kira ga mutane da su fito domin yin allurar rigakafin cutan a ko ina a fadin jihar.”