CUTAR HAWAN JINI: Illoli 6 da cutar ke yi wa dan Adam, da hanyoyi 6 da za a iya gujewa kamuwa da ita

0

Wasu kwararrun likitoci sun shawarci mutanen Najeriya akan yadda za su kulawa da lafiyarsu domin guje ma kamuwa da cutar hawan jini.

likitocin sun bada wannan shawaran ne a taron ranar cutar wanda a ke yi a kawace ranar 17 ga watan Mayu.

Likita Ogah Okechukwu yace cutar hawan jini na daya daga cikin cututtukan da ke yin sanadin mutum farad daya.

Bincike ya nuna cewa mazaunan yankin arewa maso yammacin Najeriya sun fi kamuwa da cutar hawan jini sannan kuma cutar ta fi kama maza fiye da mata.

Amma abin takaici shine cutar bai kyalle matasa ba musamman daga shekara 25 zuwa sama.

A wani bincike da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya tayi ya nuna cewa cutar hawan jini ta fi kama bakaken fata fiye da turawa, bakaken ma ya fi kama talakawa.

Okechukwu yace bayan bugawar zuciya da shanyewar wani sashen jikin mutum cutar na iya zama sanadiyyar mutum ya rasa ganinsa da cutar koda.

Ya kuma shawarci mutane akan hanyoyin da za su iya bi da kiyayewa domin gujewa kamuwa da cutar kamar haka:

1. Mutum ya yawaita motsa jiki domin kiba a jiki na kawo cutar hawan jini

2. A rage yawan cin Kitse, sannan a yawaita cin kayan lambu da gayyayyaki.

3. A Rage yawan

4. A rage yawan cin gishiri.

5. Shan taba sigari da shan giya na kawo cutar hawan jini.

6. A yawaita zuwa asibiti domin yin gwaji akan cutar.

Share.

game da Author