Mai ba shugaban Kasa shawara a harkar yada labarai Femi Adesina ya sanar da cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tashi zuwa kasar Britaniya yau domin ganin likitocin sa.
Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo zai ci gaba da rikon kujeran shugabancin Kasa har sai ya dawo.