Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da sako wasu daga cikin ‘yan matan Chibok 82 ta hanyar yin musanya da wadansu ‘yan kungiyar Boko Haram da ke tsare.
Buhari ya ce yana sane da tattaunawar kuma ya mika godiyarsa ga gwamnatin kasar Switzerland, kungiyar Red Cross, da wasu kungiyoyi masu zaman Kansu.
Garba Shehu ya ce yau ne ‘yan matan za su iso Abuja inda shugaban da kansa zai yi musu maraba.