Buhari ya daukeni kamar Dansa ne saboda kaunar da yake nuna mini – Inji Osinbajo

1

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yace irin kaunar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yak e nuna masa kauna ce kamr na uba da da.

Osinbajo dan shekara 60, ya fadi hakanne a fadar sarkin Katsina a wata ziyara da ya kai fadar.

“ Ina jinane kamar ina gida, domin ko yadda shugaban kasa ya dauke ni kamar dan uwansa na jinni ne.”

“ Kai bari in gaya muku ma Buhari ya na dauka nane kamar shine ya haifi, yadda uba zai rike dansa.

“ Irin ayyukan da Buhari ya bar mini inyi ya nuna akwai matukar yarda a tsanin mu sosai.

“ Ina rokon Allah da ya ba shugaban mu lafiya domin mutum ne mai son hadin kan kasa da kishin ta.”

Share.

game da Author