A halin yanzu Shugaba Muhammadu Buhari ya na samun sauki sosai duk da dai likitocin sa ne kadai za su iya bayyana ranar da ya dace ya koma Najeriya. Wata majiya ce a Ofishin Jakadancin Najeriya a Landan ta bayyana wa Premium Times cewa Buhari na samun sauki kwarai da gaske.
“Mun gode wa Allah, domin shugaban kasa ya warware sosai, kuma ya kara samun kuzari, to amma likitocin sa ne kadai za su iya bayyana lokacin da ya kamata ya koma Nijeriya.” Inji majiyar Premium Times.
Jami’in kuma majiyar mu, wanda ke zuwa wajen Buhari a kullum, ya nemi a sakaya sunan sa, domin ya ce ba shi da hurumin da zai yi magana da ‘yan jarida.
Buhari dai ya bar kasar nan ranar 7 Ga Mayu, 2017 domin a ci gaba da duba lafiyar sa a Landan. Idan za a tuna ya dawo ne a cikin watan Maris, 10 ga wata bayan shafe kusan kwanaki 50 da ya yi a tafiya ganin likita ta ta frko a cikin watan Janairu.
Bayan dawowar sa, ya bayyana cewa ba da dadewa ba zai sake komawa London domin a kara duba lafiyar sa. Ya kara da cewa tun da ya ke bai taba rashin lafiya irin wannan ba, kuma ba ya jin an taba yi masa karin jini a baya, ko lokacin da ya ke soja, sai a waccan tafiya Landan din.
Sai dai kuma ya na sake komawa Landan sai aka rika baza jita-jitar cewa ya rasu. An yada wannan jita-jitar ne a kafofin sadarwa na zamani na Facebook da whatsaApp, amma ba a jaridu ba.
Majiyar Premium Times ta nuna rashin jin dadin yadda aka rika danganta waccan jita-jita da cewa daga ofishin jakadancin Najeriya da ke Landan sanarwar mutuwar ta fito.
Da ya ke bayani a kan masu cewa shugaban kasa ya yi murabus saboda dalilai na rashin lafiya, ya ce “Wannan kuma matsalar su ce, domin Allah shi ne mai bayar da lafiya, mai kashewa kuma mai raya duk wanda ya ga dama.”