‘Yan matan Chibok da suka ki biyo ‘yan uwansu da suka dawo makon da ya gabata sun ce daya daga cikin dalilan da ya sa ba za su dawo ba shi ne yanzu baza su iya komawa addinin kirista da suke ciki a da ba.
A wannan bidiyo sun yi kira ga iyayensu da su dawo addinin musulunci.
‘yan matan su hudu na zaune ne sanye da bakin hijabi da Nikam inda na tsakiya daga cikin su wanda ta yi hirar na rike da bindiga kirar AK47.
A wata sanarwa da kakakin rundudar soji Janar SK Usman ya fitar, yace wannan bidiyo ba zaiyi tasiri ba domin gwamnati ta riga taci karfin kungiyar kuma har yanzu suna shan ruwan wuta daga dakarun ta na sama.
Yace irin wadannan bidiyoyi farfaganda ce kawai.