Gidan Jaridar BBC ta roki Sarkin Kano Muhammadu Sanusi kan kuskuren da ta yi a labarin da ta saka na badakalar kudaden masauratar Kano da aka zargi sarki Sanusi wai ya kashe su ba akan ka’ida ba.
BBC ta ce wanda ya fassara hirar da tayi da shugaban hukumar da ke binciken yadda aka kashe kudaden masarautar Mahyi Magaji ne bai yi dai-dai ba inda kuma su a can kasar Britaniya suka wallafa shi a zamman dai-dai ne.
Babban Darektan Editocin BBC Jamie Angus ne ya sanar da hakan a wasikar da BBC din ta rubuta wa Sarki Sanusi inda yace BBC ya rubuta wa sarkin wasika ta musamman domin neman ya yi hakuri akan kuskuren da su kayi.
“ Bayan an gudanar da hirar, an mika ma wani abokin aikin mu ne a ofishin mu dake Abuja domin ya fassara kafin aka aiko dashi Landan”
Bayan mungudanar da bincike akai sai muka gano cewa abinda muka rubuta ba daidai bane da abinda shi Muhyi ya fadi a hirar tasa in da shi da kansa ya sanar mana cewa ba’a gaiyace ka ba a zaman kwamitin dake binciken wannan badakala.
“ Abinda muka rubuta cewa wai kaima za’a bincikeka lallai ba haka bane kuma muna rokon ka da ka yi hakuri.” Jamie Angus