Barayin da suka sace Dan majalisar wakilai Garba Durbunde a hanyar Abuja zuwa Kaduna sun sake shi da yamman Laraba.
Masu garkuwa da mutane sun sace da Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Sumaila da Takai na jihar Kano, Honorabul Garba Durbunde a hanyarsa ta zuwa Kano daga Abuja.
Premium Times ta ji cewa an yi garkuwa da shi ne kafin ya kai garin Jere, a kan hanyar sa ta zuwa Kano a ranar da abin ya auku.
Mai magana da yawun majalisa, Hon. Namdas ne ya sanar wa PREMIUM TIMES haka in da yace Durbunde ya na tare da iyalansa a yanzu hakan.