Bara da Almajirai suke yi ba Musulunci bane – Sarkin Musulmai

0

Sarkin Musulmai Abubakar Sa’ad ya ce barace-barace da Almajirai suke yi a tituna da unguwannin mu ba musulunci.

Dr. Sa’ad ya fadi haka ne a wajen taron Jama’atu da akeyi duk shekara domin tattaunawa kan shigowar watan Ramadan da ake sa ran za ta kama a karshen makonnan.

Dr. Sa’ad ya ce irin barace-baracen da Almajirai suke yi ba musulunci bane kuma ya kamata a nemo hanyoyin da za a bi domin dakatar da shi a tsakanin mutane.

” Musulunci ya na kira ne ga mutane da su tashi su nemi na kansu da kuma hana zaman kashe wando amma ba wai ayi amfani da addini ba ana abin da ba haka ba kamar bara ko roko.

Yayi kira ga attajirai da su tsarkake dukiyoyinsu wajen bayar da zakka sannan kuma ya roki gwamnati da ta samar wa matasa ayyukan yi domin gujewa fadawa irin wannan mummunar aiki.

Share.

game da Author