Babu wanda na sa ya sanar da shiri da nakeyi wa siyasa, karya shu
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya karyata shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jiharsa da yace wai shi El-Rufai ba zai yi takarar gwamna ba a 2019 sannan kuma wai wani dan kasa da shekara 50 ne zai tsayar ya kuma mara wa baya domin zama gwamnan jihar.
El- Rufai ya ce baya bukatan wani ya ari bakinsa ya ci masa albasa.
” Idan lokaci yayi da kai na zan fadi abin da na shirya wa kai na amma ni ban sa wani yayi shela akai na ba.
” Game da abinda shugaban ma’aikatan fadar gwamnati ya fadi, ya fadi ra’ayinsa ne amma ba daga baki na hakan ya fito ba. Ni bani da ra’ayin tilasta wa mutane abinda ba sa so. Kuma babu wani mutum da zai kirkiro wani abu da ba ya cikin kundin tsarin mulkin kasa ko na zabe da za abi, domin saba wa doka ce.
“Duk da cewa gwamnatin mu zata ci gaba da ba matasa dama domin koyan yadda ake gudanar da mulki, ba za mu tilasta wa jama’a dole sai mulki ya koma ga matasan ba.
El-Rufai ya umurci ma’aikatar KASUPDA da ta cire duk wani hoton dan siyasa ko na wani dan takara a gine-gine da titunan jihar domin wai ba a riga an buga gangar siyasa ba tukuna.
Sannan kuma ya ce duk wani jami’in gwamnati da aka ga yana hakan za a sauke shi daga kujeran sa.
” Saboda haka ina rokon duk wani jami’in gwamnati da ya yi takatsantsan akan hakan.
Discussion about this post