Kotu a Abuja ta ba da umurnin ci gaba da ajiye tsohon ministan Abuja Bala Mohammed a kurkukun Kuje har sai ranar Juma’a.
A na tuhumar Bala Mohammed da karbar cin hanci na naira miliyan 500 a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya, Abuja.
Alkalin Kotun Abubakar Talba yace za a ci gaba da sauraron neman belin da lauyoyin ministan suka shiagar a kotun ranar 12 ga watan Mayu.