Kungiyar likitocin Najeriya sun ki amincewa da shirin gwamnati na mayar da albashin ma’aikatan asibiti bai daya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a taron kungiyar da akayi a jihar Cross Rivers shugaban kungiyar Mike Ogirima yace duk da cewa ma’aikatan kiwon lafiya a fadin Kasa Najeriya na fama da matsaloli da mayar da albashin likitoci da sauran ma’aikatan asibitin ya zamo bai daya bai dace ba saboda a ganinsu likitoci sun fi sauran ma’aikatan asibiti aiki.
Ya kara da cewa ba wai su likitoci suna ja da wannan shiri bane kwata-kwata abinda suke kira da ayi shine kada gwamnati ta mai da albashin duka ma’aikatan ya zamo bai daya.
“ Za’a iya yi musu kari amma dayake ko wa da irin nashi kwarewar sannan su likitoci su ne ke gaba da sauran ma’aikatan asibitin bai kamata ace wai an mai da albashin bai daya ba da sauran.”
Bayan haka kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta yi kokarin gyara asibitocin kasa Najeriya musamman abinda ya shafi wadatasu da magunguna da gine-ginen da wasu ke bukata.
Bayan haka kuma ta shawarci gwamnati da ta kafa wata kungiyar kwararrun likitoci da za su dinga bada shawarwari da zai sa a samu ikon iya ganowa da toshe duk wata kafa da zaiyi sanadiyyar bullowar wata cuta a kasar.
Yace hakan zai taimakawa gwamnati wajen gano hanyoyin da ya kamata abi kamar yadda ta dukufa wajen kirkirowa da sarrafa sabbin magungunan rigakafi a kasa Najeriya.
Kungiyar ta koka da yadda gwamnati ta yi burus da bibiyan gano bakin zaren tun lokacin da cutar sankarau ya bullo a kasa kafin ya nemi fin karfin gwamnatocin jihohin da cutar yayi wa illa.
Daga kashe kungiyar ta ce za ta kirkiro da dokar da zai samar wa kowani kwararren likita tambari da hakan zai taimaka wajen kau da baragurbin likitoci a tsakaninsu.