Mene ne Ma’anar kalmar “Azumi” – As-saum ko Siyam – a larabci?
Azumi a yaren Larabci, shi ne kamewa daga barin wani abu, karma kamewa daga barin Magana ko ci, ko sha.
Mene ne Ma’anar Azumi a Shari’a?
Ma’anar Azumi a Shari’ance, wata Ibada ce ta hanyar kamewa daga cin abinci da abin sha da jima’i, tun daga hudowar alfijiri har zuwa faduwar rana da niyyar bautar Allah SWT.
Mene ne Hukuncin Yin Azumi a Musulunci?
Azumin da Allah ya shar’anta ya kasu zuwa ga:
1 – Azumin Wajibi – Ya kasu gida biyu :
A – Azumin da Allah ne ya wajabta a kan bawa tun da farko, shi ne azumin watan Ramadan.
B – Azumin da bawa ne yake sababin wajabata wa kansa shi, kamar azumin bakance, da azumin kaffara.
2 – Azumin Nafila
Shi ne dukkan azumin da shari’a take so a yi shi, kamar azumin ranar Litinin da Alhamis, da azumin kwana uku a kowane wata, da azumin ranar Ashura, da azumin goman farko a cikin watan Zulhijjah, da azumin kwana shida a cikin watan Shawwal da azumin ranar Arafa.
Mene ne Hikimar Shar’anta Azumi a Musulunci?
1 – Tabbatar da tsoron Allah, wajen amsa umarninsa, da biyayya ga shari’arsa. Allah Madaukakin Sarki ya ce, “(An wajabta muku azumi ne, ko kwa samu tsoron Allah” (Albaqara : 183).
2 – Sabawa mutum da kyautatawa, da jin tausayin mabukata da talakawa, saboda idan mutum ya dandani yunwa zuciyarsa za ta yi laushi ta karkata zuwa ga taimakon mabukata.
3 – Sabawa kai hakuri, da karfafa wa zuciya wajen danne sha’awata.
4 – Samarwa jiki hutu da lafiya a cikin azumi.
Mene ne Falalar Mai Azumi?.
Azumi rukuni ne daga cikin rukunnan musulunci, yana da falala mai girma, da lada mai yawa, yana sanya Imani da Takawa, Kuma karkuwa ne daga wuta, kariya ne daga sha’awa. Allah Yana bada lada wanda ba shi da iyaka ga mai azumi kuma ya gafarta zunuban sa.
Hadisi ya ingata daga Abu Hurairata (Allah ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah ( SAW) ya ce, “Dukkan aikin dan Adam ana ninka masa shi, ana ninka kyak-kyawa sau goma, har zuwa ninki dari bakwai. Allah Mai girma da buwaya ya ce, “Sai dai azumi, hakika shi nawa ne, ni ne nake ba da ladansa, mutum yana barin sha’awarsa da abincinsa saboda ni. Mai azumi yana da farin cikin biyu, farin ciki yayin bude bakinsa, da farin ciki yayin haduwa da Ubangijinsa. Warin bakin mai azumi ya fi almiski kanshi a wurin Allah” [Bukhari da Muslim] .
An ruwaito daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, Allah mai girma da daukaka ya ce, dukkan ayyukan dan Adam nasa ne, amma ban da azumi, domin azumi nawa ne, kuma ni ne zan yi sakayya domin azumi garkuwa ne, duk ranar da mutum yake yin azumi baya zina, baya daga murya, kuma ba ya yin wauta kuma idan wani ya zage shi, ko ya neme shi da fada lallai ya ce, ni ina yin azumi (sau biyu) Manzon Allah (SAW) ya ce, na rantse da wanda raina yake hannunsa, warin bakin mai azumi ya fi kamshi a wajen Allah ranar kiyama daga kamshin turaren Almiski, kuma mai azumi yana da farin ciki guda biyu da zai yi farin ciki da su, lokacin da yake yin buda baki, zai yi farin ciki da lokacin da zai hadu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa. (Bukhari da Muslim).
An karbo daga Sa’ad (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, lallai a cikin aljanna akwai wata kofa ana kiranta Arrayyan, babu wanda zai shige su sai mai azumi, Za’a ce ina masu azumi? Sai su mike, sai a ce babu wanda zai shige ta wanda basu ba, idan suka shiga sai a rufe kofar aljannar. Ba mai shiga wannan kofa ta Arrayyan sai masu azumi, (Bukhari da Muslim).
Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce, duk wanda ya azumci watan Ramadana yana mai Imani, yana mai neman lada, to, an gafarta masa zunubansa wanda ya gabatar (Bukhari da Muslim).