Majalisar dattijai ta karbi rahoton kasafin kudina 2017 daga kwamitin kasafin kudin majalisar.
Shugaban kwamitin Sanata Danjuma Goje ne ya mika rahoton a zauren majalisar yau Talata.
Shugaban Majalisar Sanata Bukola Saraki ya nuna jin dadinsa da taya mambobin kwamitin murnar kammala aiki akan kasafin kudin.
Ya ce za a gabatar da abin da kasafin kudin ya kunsa ranar Alhamis mai zuwa wato jibi Kenan sannan za a raba takardun bayanai kan kasafin kudin ga ‘yan majalisar.
Saraki ya kara da cewa majalisar zata sanar da dukkan abinda kasafin kudin ya kunsa ga ‘yan Najeriya.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika kasafin kudin 2017 tun a shekarar 2016 amma samun amincewa majalisa bai yiwu sai yanzu da ake kyautata zaton aski ya zo gaban goshi.
Ko daya ke shugaban kwamitin kasafin kudin na majalisar Sanata Danjuma Goje ya koka da samun matsala akai ne saboda farmakin da ‘yan sanda suka kai gidan sa inda yace sun tafi da wasu takardu da ya kunshi bayanai akan kasafin kudin.
Ana sa ran za a mika kasafin kudin nan ba da dadewa ba.
Buhari ya gabatar da kudurin kasafin kudi na sama da naira tirilyan 7 ne a matsayin kasafin kudin 2017.