Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu nasarar kwato kambun sarautar Laliga da Barcelona take rike dashi yau bayan ta lallasa Malaga da ci biyu ba ko daya a garin Malaga.
Dama can Madrid na bukatar ta buga kunnen doki ne kawai amma sai abin ya wuce haka.
Duk da Barcelona to lallasa Eibar da ci 4 da biyu samun nasarar da Madrid tayi ya sa sun zama yan kallo.
Leo Messi ne ya ci kyautar wanda ya fi kowa cin kwallaye a wannan shekarar kwallo na Laliga.
Madrid na da sauran wasa daya a gabanta shi ne na cin kofin zakarun nahiyar tura.
Zata kara ne da Juventus na kasar Italiya ranar 3 ga watan Yuni.
Ita ma Barcelona zata kara da Deportivo Alaves domin ci kofin ‘copa Del Ray’.