An zargi wasu makiyaya da kashe Sufeton ’Yan Sanda a Jihar

0

Rundunar ’yan sandan Jihar Delta, ta bayyana cewa wasu da ake zargin makiyaya ne, sun kashe Sufeton ’Yan sanda a yankin Abraka, cikin karamar hukumar Ethiope ta Gabas da ke cikin jihar.

Jami’in yada labarai na rundunar ‘yan sandan, Andrew Aniamaka ne ya tabbatar fa afkuwar kisan, a lokacin da ya ke ganawa da ‘yan jarida, ranar Larabar da ta gabata.

Ya bayyana cewa Aniamaka da wasu jami’an ‘yan sanda uku na yin sintiri ne kan titin jirgin kasa, a lokacin da makiyayan da ake zargin suka yi masu kwanton-bauna.

Sauran ’yan sandan uku kuma duk sun ji raunuka a jikin su.

“Kwanton-bauna aka yi wa jami’an mu can wajen hanyar-dogo a Abraka, inda makasan suka bude musu wuta. Abin ya zo musu cikin rashin zato, kuma aka yi ta bude musu wuta ta yadda suka kasa samu sukunin maida martani.”

Ya ce Sufeto daya ya rasa ransa, yayin da wasu uku kuma suka sami munanan raunuka. “Wannan shi ne halin da muke ciki, kuma mu na kan kokarin bin sawun ganowa da kamo wadanda ake zargin aikata harin.”

Share.

game da Author