Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sanar da cewa dakarun sojin Najeriya sun tsinto wata ‘yar makarantar Chibok da ke tsare a hannun Boko Haram a dajin Sambisa.
Osinbajo ya fadi haka ne a taron mako-mako da majalisar zartaswa keyi.
Yace ya yi Magana ba babban hafsan sojin Najeriya, kuma ya tabbatar masa da haka.
An kawo ta Abuja wajen sauran ‘yan matan.
Bayan haka kuma yayi kira ga mutanen kasa Najeriya da suyi watsi da zantukan da ake ta yada wai Boko Haram suna sake sabon shiri domin yin wata sabuwar yunkuri a dajin Sambisa.
Yace Dakarun sojin Najeriya a shirye suke da su murkushe duk wata barazana da wani kungiya take kokarin yi a kasar.
“ Idan suka ce zasu dawo su hadu kuma domin tada da wata masifar, mu kuma a shirye muke da mu watsa su”