Jami’an ‘yan sanda dake unguwan Ka’oje, Bagudo jihar Kebbi sun kama wani magidanci dan shekara 37 mai suna Danbaba Umaru yana kwakule wasu sassan wani gawa a makabartar yankin.
Danbaba dai yakan yi haka ne domin siyarwa ga matsafa wanda sune sukan turo shi.
Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kebbi, Ibrahim Kabiru, yace sun kama Danbaba ne bayan samun bayanan sirri akan yana aikata hakan.
Yace Danbaba ya sanar wa ‘yan sandan cewa wani ne mai suna Muhammed mazaunin jihar Sokoto ya aikeshi da ya samu masa wasu sassan mutum.
Danbaba yace wannan shine karonsa na farko da ya aikata hakan.
‘ya’yansa 10.