Shugaban hukumar da ke binciken badakalar kashe-kashen kudi da ta keyi wa masarautar Kano, Muhyi Magaji ya sanar da cewa hukumarsa ta dakatar da binciken.
Gwamnatin jihar Kano na tuhumar fadar Sarkin Kano da kashe kudaden masarautar ba tare da bin ka’ida ba.
Muhyi ya ce hukumar sa ta dakatar da haka ne ganin majalisar dokokin jihar ita ma ta bude fai-fai fara binciken masarautar.
Majalisar dokokin jihar a zamanta na makon da ya gabata ta sanar da kafa wata kwamiti na musamman domin binciken zargin da akeyi wa fadar sarki Muhammadu Sanusi kan kashe kudaden masarautar ba ta hanyar da ya kamata ba.
” Ba za mu ci gaba da gudanar da binciken da mukeyi wa masarautar Kano ba saboda majalisa ita ma za ta yi irin haka.
” A ganin mu bai kamata ace wai munayi majalisar jihar ma tana yi ba.
Dalilin haka ya sa muka dakatar da namu su su ci gaba kawai.