Aisha Buhari ta tafi kasar Britaniya duba Buhari

0

Uwargidan shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari a safiyar Talata ta bar kasa Najeriya zuwa kasar Britaniya domin ta ziyarci mijinta.

Aisha ta tashi ne daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja.

Kafin ta shiga jirgi ta zanta da manema labarai inda ita mika godiyarta ga ‘yan Najeriya saboda adu’o’in da sukayi tayi wa mijinta na neman Allah ya bashi lafiya mai dorewa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar kasa Najeriya ranar 7 ga watan Mayu domin ganin likitocin sa da suke duba lafiyarsa a kasar Britaniya.

Share.

game da Author