A fara duban watan Ramadan daga gobe Juma’a – Sarkin Musulmi

0

Sarkin musulmi Abubakar Sa’ad yayi kira ga musulman kasa da su fara duban watan Ramadana daga ranar 26 ga watan Mayu, wanda yayi daidai da 29 ga watan Sha’aban 1438 AH.

Wani babban jami’I a fadar sarkin Musulmin Sambo Wali ne ya sanar da haka a wata takarda da ya fito daga fadar.

“ Ana kira ga musulman kasar nan da su fara duban watan Ramadan daga gobe Juma’a 26 ga watan Mayu. Duk wanda ya ga watan kuma ya sanar da Mai’anguwa, dakaci ko hakimin garin su domin sanar wa sarkin Musulmi.

Ga lambobin da za’a kira kamar haka: 0803-715-7100, 0706-741-6900, 0806-630-3077, 0806-548-0405, 0803-595-7392, 0803-596-5322 da 0803-614-9767.

Share.

game da Author