A biya mu alawus din mu tunda wuri – Dakarun Sojin Bataliya na 38

0

Dakarun soji da suka dawo daga aikin samar da tsaro na kasa da kasa a kasar Liberiya dake karkashin Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya sun rubuta wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasikar neman ya saka baki a biyasu hakkinsu da rundunar soji ta kasa taki biyansu har yanzu.

Dakarun bataliya 38 sun dawo kasa ne tun a watan Faburairun 2017 bayan kammala aikinsu a kasar Liberiya.

” Muna kira ga Buhari da ya matsawa shugabannin Sojin kasa su biya mu hakkokinmu tun da wuri domin idan ba haka ba zamu dauki mataki akai wanda hakan ba zai yi wa kowa dadi ba.

” Mun dawo tun watan Faburairu na wannan shekara amma har yanzu shiru kakeji babu wani magana akan biyan mu kudaden mu bayan mun Sani cewa majalisar dinkin duniya ta biya kudaden tun tuni.

” Mu ba za muje majalisar dokoki na kasa ba domin nuna fushin mu.

Daga karshe dakarun Sojin sun roki shugaban Kasa da ya karkato da akalar sa na yaki da cin hanci da rashawa zuwa rundunar Sojin Najeriya.

Share.

game da Author