Babban dan kwangilar da ke aikin titin jirgin kasa na kai-da-kawo da zirga-zirgar jirgin a Abuja, ya bayyana wa Ministan Abuja, Muhammad Bello cewa za a kammala aikin titin jirgin kasan nan da watan Oktoba mai zuwa, yayin da za a fara gwada hawan titin a cikin watan Nuwamba.
Ministan ya bayyana wa wata tawagar kungiyar masu kula da harkokin yawon bude ido ta kasa wannan bayani ne yayin wata ziyara da suka kai masa.
Kungiyar a karkashin jagorancin shugaban ta Tomilola Akingbogun ne suka kai wa ministan ziyara a ofishin sa da ke shiyyar Garki 1, Abuja.
Ministan ya ce kamar yadda ya samu tabbaci daga dan kwangilar da ke aikin, za a fara zirga-zirga ka’in da na’in a cikin watanni uku na farkon shekara ta 2018.
Ya kuma ce an kafa kwamiti domin ya duba matsalar karbar haraji a Abuja sannan yayi kira da a yawaita gina kananan dakunan baki masu arha saboda yawan baki da suke shigowa garin Abuja.
Ya ce samun gudanar da ayyukan masu masana’antun kansu da sauran nau’o’in hada-hadar kasuwanci a Abuja, abu ne mai muhimmanci, don haka za su gaggauta duba matsalar yawan tsawwala haraji a cikin babban birnin tarayya.
A karshe ya ce tilas a ba harkokin yawon bude ido muhimmanci a Abuja domin a samu walwala da sukunin tafiyar da su.