’Yan Kasuwa a jihar Adamawa sun koka da rushe musu shaguna saboda zuwan Osinbajo

1

Kananan ‘yan kasuwar a Yola sun koka da rushe musu shaguna da ke a gefen titunan jihar. An dai rushe shagunan na su ne domin kara wa garin Yola kyau, yadda zai kayatar a yayin ziyarar da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya kai a Alhamis din nan.

Wasu ‘yan kasuwa da suka zanta da Premium Times, sun yi korafin cewa wannan abu da gwamnatin jihar Adamawa ta yi musu, ba wai abu ba ne sai tsantsar mugunta da keta kawai.

“Mu dai wannan ziyara da Osinbajo zai kawo a Yola, bala’i ne a gare mu, ba alheri ba. Sun ruguza mana kantuna, sun kuma raba mu da harkokin kasuwancinmu.” Haka wani dan tireda mai suna Vandi ya bayyana was PREMIUM TIMES.

Vandi ya ce su na kallon wannan aika-aika ta rushe musu shaguna tamkar mafarki, domin a tunanin su, gwamna Jibrila Mohammed ba zai taba daukar wani mataki na kuntata wa kananan ’yan kasuwa ba, ganin cewa shi ma ya taba yin kasuwancin a baya.

Shi kuwa shugaban masu sayar da kayan marmari da kayan miya na jihar, Abubakar Maidama, ya koka cewa gwamnati ba ta nemi jin ta bakin su ko shawara da su ba kafin ta rushe musu shaguna. Ya ce ko da kkyakkyawar matufa aka yi rusau din, to ya kamata a tuntube ta.

Maidama ya kara da cewa wannan aika-aika da gwamnatin Bindow ta yi zai harfar da marasa aikin yi, sannan a samu karin aikata laifuka, saboda an rushe wa jama’a shaguna a daidai lokacin da kowa ke ta fafutikar yadda ma zai iya ciyar da kan sa da iyalansa.

“Da a ce gwamnati ta tuntube mu kafin ta rushe mana shaguna, to da mun bayar da shawara da gudumnawar yadda za a magance matsalar. Amma a zamani irin wannan haka kawai gwamnati ta tashi da sanyin safiya ta fatattaki mambobinmu masu kananan sana’o’i, to a gaskiya abin dubawa ne.

Wani hasalallen dan tireda da abin ya shafa, ya nuna takaicin sa cewa an nuna son kai wajen rushe shagunan mutane, an ki ruguje na wasu, an ruguje na wasu. Didike ya ce in da abin na su akwai gaskiya a ciki, me ya hana su rushe na wasu ‘yan jam’iyyar da ke mulki ne?

“Shin wai don kawai Mataimakin Shugaban Kasa zai zo Adamawa sai a bi a rushe shagunan wadanda suka zabe shi, a raba su da kasuwancin su?

Sai dai kuma Kwamishinan Gidaje da Tsara Birane, Abubakar Magaji, ya ce sun yi abin da suka yi a bisa doka da oda.

Ya yi kukan cewa ai akwai dokokin da suka bayar da iznin yin gini ko kafa shaguna a gefen titi, wadanda dole a bi su don kada a toshe hanyoyin ruwa da kwalbatoci.

Ya kuma ce ‘yan tiredar zu na zubar da shara a kan titi yadda ta ke lalatawa da kuma toshe sabbin kwalbatoci da gine-ginen da gwamnati ta yi.

Share.

game da Author