Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya kalubalanci gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da ya bada bayanai akan yadda suma gwamnoni suke kashe kudaden kananan hukumomin jihohinsu da na asusun tsaro.
Dogara ya fadi hakan ne a wajen rufe wata taron da ya halarta a Kaduna.
“ Ina kalubalanta El-Rufai da shima ya fito ya sanarwa mutanen jiharsa yadda gwamnatinsa take kashe kudaden kananan hukumomi da kudaden asusun tsaro. Idan yayi haka ka ga kowa sai yabi sahu.
El-Rufai ya yi kira ga majalisar kasa da ta sanarwa duniya kasafinta da yadda take kashe su.
“ Idan da zasu fito su gayawa duniya kudaden da suke kashe wa na tsaro duk wata da na kananan hukumomi da hakan zai sa kowa ma ya fara kokarin bin sahun su.
Daga karshe Yakubu Dogara yace matsalolin da ake samu akan da majalisar kasa shine na rashin sanin yadda take gudanar da ayyukanta.