An dade masana musamman a fannin kiwon lafiya na ta yin fashin baki kan rashin ingancin amfani da wadansu daga cikin magungunan da mutane ke amfani da su wajen maganin cutar Zazzabin cizon sauro musamman wanda aka fi sabawa da shi wato Chloroquine.
A ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro na wannan shekara, Ministan kiwon Lafiya, Isaac Adewale ya gargadi mutane da su nisanta kansu daga amfani da maganin Chloroquine domin kawar da cutar.
Ya ce maganin ba na cutar bane.
Adewale ya fadi hakan ne yayin da yake bada jawabinsa a taron inda ya shawarci mata masu dauke da juna biyu cewa a duk lokacin da suka ziyarci asibiti domin yin awo su tabbata sun karbi maganin maleriya wanda ake kira da Sulphadoxine-Pyrimethamine (SP) wanda zai taimaka musu dana jirajiran su.
Ya ce bincike ya nuna cewa kashi 90 bisa 100 na mutanen Najeriya na cikin hadarin kamuwa da cutar maleriya domin cutar ya kawo mutuwan kashi 30 bisa 100 na yara, ya kuma kawo ajalin kashi 25 bisa 100 na yara kanana ‘yan kasa da shekara daya sannan kuma cutar ta kashi 11 bisa 100 na mata masu dauke da juna biyu.
Ya kuma kara da banda kisan mutanen da cutar ke kawowa cutar na kawo wa mata masu dauke da juna biyu wasu matsaloli kamar bari, haiho dan da bashi da nauyin da ya kamata da kuma makamantansu.
Bayan haka shekaru 11 kenan da kasa Najeriya ta sanar da hana amfani da maganin cutar zazzabin cizon sauro mai suna chloroquine saboda bayanan da kwararru suka bada cewa maganin na da illa sannan kuma baya warkar da cutar zazzabin cizon sauron.
A dalilin haka gidan jaridar PREMIUM TIMES ta gudanar da wata bincike akan ko mutane sun guji maganin ko kuma suna nan suna amfani dashi domin warkar da cutar.
Sakamakon binciken ya nuna cewa har yanzu fa mutane na yin amfani da maganin domin warkar da cutar zazzabin cizon Sauro idan sun kamu.
Kamar yadda bincike ya numa, a shekarar 2005 ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa ta hana amfani da maganin bayan hukumar kiwon lafiya na dinkin duniya ta shawarce ta akan hakan.
Dalilin da ya sa kasa Najeriya ta yi hakan shine ganowan da akayi cewa maganin baya warkar da cutar zazzabin cizon sauro duk da cewa maganin na warkar da wasu cututtuka.
Hukumar kula da abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC ta ce tana yi wa maganin rajista domin a binciken ta ta gano cewa maganin na warkar da wasu cututtuka da ba zazzabin cizon sauro ba.
Da muka yi hira da wani ma’aikacin kamfanin sarrafa magani na ‘Dana Pharmaceuticals’ ya ce har yanzu kamfanin Dana din na sarrafa maganin chloroquine amma ba don warkar da cutar zazzabin cizon sauro ba sai dai don wasu cututtukan da suka gano yana warkar wa.
Ya ce duk da haka ba za a rasa mutanen da ke amfani da maganin ba domin warkar da cutar zazzabin cizon sauro ba.
Gidan jaridar PREMIUM TIMES ta tambayi darektan aiyuka da sadarwa na hukumar NAFDAC Abubakar Jimoh ko suna yi wa maganin rajista a hukumar tasu har yanzu.
Jimoh yace hukumar NAFDAC din na yi wa maganin rijista har yanzu.
Ya ce dalilin da ya sa suke yi wa maganin rajista shine domin maganin na warkar da wasu cututtuka kamar cutar ciwon kafa wanda ake kira da turanci ‘Rheumatoid Arthritis’ sannan kuma da wasu cututtukar dake kama hanjin mutum.
Adewole ya ce a kowace shekara kasa Najeriya na kashe kudaden da ya kai Naira biliyan 300 wajen ganin cewa ta kawar da cutar maleriya daga kasan amma har wa yau abi ya ki ci ya ki cinyewa.
Duk a dalilin neman samun mafita akan hakan a dan kwanakin nan ne Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya wato ‘WHO’ ta sanar da cewa kamfanin GlaxoSmithKline (GSK) na kasar Britaniya ta sarrafa wata sabuwar allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro mai suna “Mosquirix”.
Kungiyar ta ce a sakamakon haka za ta gwada ingancin maganin a shekaran 2018 akan musamman yara kanana daga shekara biyar zuwa kasa a kasashen da suka fi kamuwa da cutar Zazzabin cizan sauron.
Kasashen kuwa sun hada da Ghana, Kenya da Malawi.
Wani jami’in hukumar mai suna Matshidiso Moeti yace dalilin da ya sa kungiyar ta shirya yin hakan shine don jarraba ingancin maganin kafin a baza shi a sauran kashen duniya da ke bukatar irin wannan taimako.
Moeti ya ce maganin zai taimaka wajen ceto rayukan mutane da dama a kasashen Afirka din.
Wasu masu jawabin da aka gaiyata zuwa taron kamar jami’ar kiwon lafiya na tarayya Evelyn Ngige da kuma shugaban kwamitin shirye-shiryen kawar da cutar maleriya Obi Adigwe sun amince da cewa kamata ya yi mutanen kasa Najeriya su hada hannu wajen kawar da cutar daga kasan gaba daya.
Sun kuma kara da cewa gwamnatin kasa ya kamata ta su zubi da dama musamman bagarorin sarafa magunguna domin sami makamin kawar da cutar daga kasan.
Adewole ya ce kowani dan kasa Najeriya na da nashi /nata rawan da za su taka wajen kawar da cutar a kasan.
Ya ce idan mutane na tsaftace muhallin su kasan za ta sami sauki wajen rage yaduwar cutar.