Yadda gwamnati ta raba kujerun aikin Hajjin bana ga Jihohin kasar nan

0

Kasar Saudi Arabiya ta kara yawan kujerun da ta ke ba kasa Najeriya daga 76,000 zuwa 95,000.

Saboda wannan kari da aka samu hukumar kula da aikin Hajji ta kasa ta raba kujerun ga jihohin kasar nan kamar haka:

Abia 62, Adamawa 2,097, Akwa Ibom 60, Anambra 63, Bauchi 3,213, Bayelsa 81, Benue 390, Borno 2,786, Cross River 60, Delta 107, Ebonyi 97, Edo 294, Ekiti 209, Enugu 65, FCT 2,657, Gombe 2,205 and Jigawa 2,677.

Sauran jihohin sun hada da Kaduna 6,327, Katsina 4,930, Kebbi 4,629, Kogi 838, Kwara 2,164, Lagos 3,957, Nasarawa 1,860, Niger 3,604, Ogun 1,353, Ondo 302, Osun 917, Oyo 1,363, Plateau 1,348, Rivers 375, Sokoto 5,571, Taraba 1,457, Yobe 2,256 and Zamfara 4,496.

Rundunan sojin Najeriya ta sami kujerun hajin 497,sannan kamfanonin shirya tafiye tafiye masu zaman kansu sun sami kujeru 20,000.

Jihar Kano ce ta samu kaso mafi yawa da Kujeru 6,602 inda jihar Imo ta samu mafi karancin kaso da kujeru 47.

Share.

game da Author