Wasu ‘yan kunar bakin wake sun kai hari a masallaci

0

Mutane biyu ne suka rasa rayukan su inda wasu biyar suka sami raunuka a dalilin wata harin bam da wasu ‘yan kunar bakin wake su ka kai wani masallaci a jihar Barno.

Rundunar ‘Yan sandan jihar Barno ta sanar cewa maharan basu sami isa cikin masallacin ba kafin su ka ta da bam din.

Harin ya faru ne a kauyen Juddumiri, dake jihar Barno.

“ Mutane da suka fito yin sallah ne suka tsare su kafin su shiga harabar masallacin inda kafin su ankara sai daya daga cikin yan matan ta ta da bam din da ke jikinta wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar ‘yar uwarta da wasu biyar da suka sami raunuka.

Share.

game da Author