Idan dai mutum yana raye ba zai gaji da ji ko ganin abubuwan al’ajabi ba.
Wannan karon kuma wata kurciya ce aka kama daure da shirgegen laya a wuyarta.
Ita dai wannan kurciya ta shafe watanni biyar tana gararamba a saririn samaniya tare da saukowa kasa don neman abinci a yankin Daganawa, karamar hukumar Bunkure dake jihar Kano.
Wasu matasa masu suna Babangida da Shehu ne sukayi ta fakon kurciyar amma Allah baiyi za su kamata ba sai yanzu.
To dama dai ita kurciya sau dayawa wadansu kan yi farautar su domin kiwo ko ci ne.
A wasu wuraren kuma akan kiwata su ne domin ayi amfani da su wajen kulla surkullen ko asiri.
Wannan dai da Babangida suka kamo anyi amfani da ita ne domin kulla asiri.
“Akwai lokacin da alumma suka yi yinkurin harbota da danko wasu da baushe duk muka hana su domin muna zaton hakan.
Cikin ikon Allah a wannan karon muka samo kalli wato tarko muka sashi a cikin gona tare da yafa tsabar gero da dawa nan take ta sauko ta kamaci har ta fada cikin tarkon inda muakayi nasarar kamata.”
Dantala Kura da ya zanta dasu kuma ya bamu wannan labari yace bayan hakane suka ga wannan shirgegen laya a wuyan Kurciyar.
Babangida da Shehu basu tsorata da ganin haka ba sai suka cire layar sannan suka warware ta.
Sun sanar da cewa an rubuta (Haihata Haihata) da jini a jikin takardan da suka warware da wadansu surkulle ajiki.
Yanzu dai Babangida da Shehu sun ajiye kurciyar suna ta bata abinci.