Tun karni na 13 harshen Hausa ya kafu a Burkina Faso – Sarauniya Ramatu

1

Sarauniyar Birnin Ouagadougou, Madam Ramatu Compoare, ta bayyana cewa harshen Hausa na daya daga cikin yaruka 63 da ake amfani da su a Burkina Faso.

Sarauniyar ta bayyana haka ne yayin da take jawabi a wurin bude Bikin Al’adun Hausawa a ranar Juma’a a Ouagadougou, babban birnin kasar.

Ta jaddada cewa tabbas harshen Hausa dadadden yare ne kuma ya na daya daga cikin yarukan da ake tutiya da shi a kasar.

Taron wanda ake gudanar da shi a Cibiyar Adana Kayan Tarihi ta Kasar, ya samu halartar wasu mashahuran masana, marubuta da kuma manazartan harshen Hausa da Nijeriya, wadanda suka hada da:

Hon. Ibrahim Birnin Magaji daga Zamfara, Dakta Bukar Usman da kuma Ado Ahmad Gidan Dabino.

Tun da farko sai da Mininstan Al’adun kasar Yacoub Campoare ya yi jawabin muhimmancin taron wajen bunkasa al’adun Hausawa da kuma kara habbaka Hausa a Burkina Faso da kuma inganta dankon zumunci tsakanin kasashen da ake magana da harshen Hausa.

tmp_7681-IMG-20170414-WA0008-1096218404

Share.

game da Author