Tsakanina da Buhari kamar da ne da Uba – Inji El-Rufai

0

Gwamnan Jihar Kaduna ya sanar wa manema labarai a fadar Shugaban kasa ranar Juma’a cewa Buhari Ubane a garesa kuma ya na matukar Alfahari da hakan.

El-Rufai yace bai ta ba samun matsala da Buhari ba kamar yadda ayi ta yadawa a kafafen yada labarai.

Ya ce dalilin da yasa baya ziyartar Buhari akai akai yanzu shine domin ganin cewa shugabn kasan na bukatar hutu.

“Shugaban kasa yana bukatan lokaci sosai domin samun hutu saboda ganawa da mutane ya na daga cikin abubuwan dake gajiyar da shugaba.

“ Ni gwamna ne kuma a duk lokacin da na gana da mutane a kalla 10 a rana na kan gaji. Ba yawan takardun da zaka sa ma hannu bane ke gajiyar da shugaba, mutanen da ke shiga da fita su ne ke gajiyar da kai.

“ Bana so in takura ma shugaban kasa wajen zuwa kullum amma muna ganawa da shi.

Da aka tambayeshi ko da gaske ne ana hana shi shiga fadar shugaban kasa, El-Rufai yace babu wanda ya Isa ya hana shi shiga fadar shugaban kasa.

“ Babu wanda ya ta ba hani shiga fadar shugaban kasa kuma babu wanda ya isa ya hani zuwa ko shiga.

“ A matsayina na gwamna bani da shamaki da fadar shugaban kasa, babu wanda zai bincike ni, kawai na ga ya kamata ne in dan daga kafa domin ya samu hutun da yake bukata.

Share.

game da Author