Tsakanin Yari da Sarki Sanusi: Ka yi koyi da Marigayi Ado Bayero wajen dattaku- Inji Yari

0

Gwamnan jihar Zamfara AbdulAzeez Yari ya yi kira ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ya yi koyi da yadda tsohon Sarkin Kano Ado Bayero ya gudanar da mulkin Kano a lokacin ya na raye.

Yari ya fadi hakan ne a  martanin da ya maida wa sarkin Kano Sanusi kan maganar da yayi game da cutar Sankarau.

AbdulAzeez Yari ya yi kira ga mutane da su daina sabon Allah sannan a yawaita neman gafaransa ko ya tausaya mana ya kawo karshen cutar Sankarau da ake fama dashi wanda ba’a taba yin irin sa ba.

Jihar Zamfara ne ta fi yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar bullowar cutar zuwa yanzu.

Fadin haka ke da wuya Sarki Sanusi a jawabin sa da yayi a Kaduna ya ce abinda gwamnan ya fadi ba karantarwan musulunci bane. Ya yi kira ga gwamnan da ya nema wa mutanen jihar sa magani maimakon hada cutar da ikon Allah da ya ke yi.

Dalilin haka ne ya sa gwamna Yari ya baiwa Sarki Sanusi amsa akan abin da ya ke kiransa da yayi.

A takardar wanda mai ba gwamnan shawara akan wayar da kan mutane da yada labarai Ibrahim Dosara ya sanya wa hannu Yari ya ce maimakon Sarki Sanusi ya kirkiro hanyoyin da zai taimakawa mutanen kasar sa da irin dinbim waye wa da yake ikirarin ya na da shi ya kan bige ne da hawa manyan motoci  kawai bayan mutanensa na bukatar taimako.

Ya ce da ma can Marigayi Sheikh Ja’afar ya taba yin wa’azi ta musamman akan Sarki Sanusi inda ya ce “Sarki Sanusi makiyin addinin Musulunci ne.”

” Maimakon Sarki Sanusi ya wanke kansa akan zargin da ake masa na yadda ya wawushe bilyoyin  kudaden masarautar Kano, ya bige da kullum sai dai yace wannan gwamnan ya yi kaza wancan yayi kaza.”

Daga karshe ya roki Sarki Sanusi da ya yi koyi da tsohon Sarki Marigayi Ado Bayero wajen dattaku a matsayinsa na Sarkin babban Masarauta kamar Kano.

Share.

game da Author