TONON SILILI: EFCC ta kama naira biliyan 13 a wani gida a jihar Legas

1

A ci gaba da tonon Silili da ake ta yi a kasa Najeriya, an sake bankado wasu kudade da aka boye a wani gida a jihar Legas da a kai naira biliyan 13.

An samu dalan Amurka na miliyan 43.4 da kuma Fan din kasar Birtaniya na Miliyan 23 duk make a wani gida dake Ikoyi, jihar Legas.

Gaba daya kudin an kiyas tasu akan Naira Biliyan 13.

Hukumar EFCC ta ce ta samu nasara gano inda wadannan kudade suke ajiyene bayan wani dan tonon silili ya sanar da hukumar a Jihar legas.

Wani Makwabcin gidan da aka samo wadannan kudade yace sun dade suna ganin wata mata na shigowa gidan da jakukkuna.

Hukumar tace da suka isa gidan mai gadin gidan yace babu masu zama a gidan sai dai wasu sukan zo gidan bayan dan kwanaki.

Share.

game da Author