TATTAUNAWA: A-tare-a-buge masifa ce kan  ‘yan siyasa – Sanata Ida

0

Sanata Ibrahim Ida tsohon Sanata ne tsakanin 2007 zuwa 2011, daga Jihar Katsina a karkashin jam’iyyar PDP. Tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya kai har mukamin sakataren dindindin a Ma’aikatar Tsaro, ofishin kula da tattalin arziki na fadar Shugaban Kasa da kuma Hukumar Tattara Rarar Ribar Man Fetur, PTF. A wannan hira da ya yi da PREMIUM TIMES, ya bayyana batutuwa da dama, ciki har da matsalar a-tare-a-buge da matasa suka fara yi wa wakilan su.

PT: Kwanan baya ka canja shekara daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Ko kayen da ku ka sha a 2015 ya gigita ka kuma ya ba ka mamaki?

IDA: Da farko dai zan iya cewa kayen da PDP ta sha a 2015, wani bala’i ne da tuni  mun san hakan za ta kasance saboda wasu dalilai da dama. Na farko dai ka ga jam’iyyar da ita kan ta gwamnatin lokacin sun shiga rudu hauragiyar rigingimu.

Na biyu, ‘yan siyasa sun nisanci al’ummar da suka zabe su, haka ita ma gwamnati ta kyamaci wadanda suka zabe ta su talakawan.  Na uku, shugabannin PDP sun kau da kai ga ainihin matsalolin da suka dabaibaye shuhabancin jam’iyyar.

Ina ganin hakan ita PDP  ta rika kallon cewa saboda ta na rike da mulki shekara sha shida, ta rika yaudarar kanta cewa sai ta yi shekara sirrin ta na mulki. To sai suke ganin saboda mulki na hannun su, idan suka rike kafafen yada labarai ya ishe su yin yadda suke so.

Abin takaici ga PDP, maimakon ta lura cewa jam’iyyun da adawar da ba a ganin karfin  kowace, idan ta na ita kai, to muddin suka hada karfi wuri guda za su iya zama gagarabadau.

Bayan sun hada karfin wuri daya, sai kuma suka kwashe wasu hwamnoni daga cikin PDP. Kada ka manta kuma, a tsari karfin jam’iyyar PDP ya na wurin kowane gwamna, a hannun sa dukkan harkokin jam’iyya suke.

Yayin da jam’iyyun adawa suka dunkule wuri daya, sai suka fito haikan su na yada farfaganta a kan PDP. Kowace matsala su ce PDP ce ta haddasa a kasar nan. Kai, ni tun ma ana saura wata shida a yi zabe na gane cewa ta shiga tarkon da ba fitowa.

PT: Ya za ka bayyana tsarin da APC ta bi ta nada Shugaban Majalisat Dattawa, Bukula Saraki?

IDA: Bari na fada maka wani abu. Tun a tashi na farko APC ta yi babban kuskure. Mu a lokacin PDP tun kafin a kaddamat da sanatoci dama PDP ta tsara yadda wannan shi zai rike wancan. Kuma za ta sa-ido ta ga cewa lallai ba a kauce daga kan wannan tsari ba. Amma su APC sai ba su yi irin wannan tsarin ba a 2015. Shi kuma Shugaban Kasa sai ya furta a fili cewa zai yi aiki da duk wanda Majalisar Dattawa ta nada a matsayin shugaba. To ni a tawa fahimta, a nan Buhari ya tafka kuskure?

PT: Wato dai a nufin ka Buhari ya tafka sagegeduwa da ya bari Bukola Saraki ya zama shugaban Majalisar Dattawa kenan ko?

IDA: Ba zan ce e ba, amma a gaskiya zan so a ce akwai sa hannun Buhari wajen nada shi Bukola din.

PT: Ga shi dai 2017 ta yi nisa, amma har yau kasafin 2017 na gaban Majalisa ana sa-toka-sa-katsi. Ba ka ganin hakan zai iya shafar kasa cika alkawurran da aka yi wa jama’a a lokacin yakin  neman zabe?

IDA: Ka lura da wani abu. Tsarin da ake bi duba kasafin kudi bai canja ba tun daga 1999 har zuwa yau. Ko a baya babu shekarar da Shugaban Kasa ya taba kai kasafi majalisa ta duba, ta mayar masa a cikin wata daya ko biyu.

Abin da za mu iya cewa shi ne bambanci kawai yadda ake bin kasafin tiryan-tiryan, ana keke-da-keke a yanzu. A baya lokacin mu ba a yin irin wannan tsatstsauran binciken, watakila za ka iya tunawa har cewa aka rika yi ma kasafin kudi a lokacin PDP duk shifcin-gizo ne. Za a kai majalisa a duba sannan a maida wa shugaban kasa. Amma abin da gwamnati za ta aiwatar ba zai kasance irin tsarin abin da kasafin ya ce a aiwatar ba ne.

Amma yanzu kuwa an zo lokacin da bangaren gwamnati ke ganin cewa abin da doka ta ce su aiwatar, shi za su aiwatar kawai. Ga kuma wani tsari mai kyau da na ga gwamnati ta shigo da shi, wato kara lokacin aiki da kasafin 2016 yadda zai ci gaba har yanzu a cikin 2017 din nan. Ka ga yin hakan zai bada damar tsayawa a tantance kasafin 2017, a sa masa hannu ya zama doka, ba tare da an samu wani tsaikon gudanar da ayyuka ba. A yanzu mu na da shugaba wanda sai abin abin da ke cikin kasafin kudi kawai zai yi aiki da shi, domin shi ne doka ta aminta a aiwatar.

PT: A farkon hirar nan ka ce PDP ta sha kaye a 2015 saboda shugabanni sun raba hanya da talakawan da suka zabe su. Yanzu kuma ga wata babbar matsala ta kunno kai, talakawa sun fara yi wa ‘yan siyasa a-tare-a-buge. Shin wannan abin damuwa ne sosai kuwa?

IDA: Wannan tambaya ta na da muhimmanci kwarai da gaske. Sannan kuma abin damuwa ne matuka. Wannan a-tare-a-buge wasu alamomi ne na rashin kyakkyawan wakilci da ake yi wa jama’a. A kan tare dan siyasa a rufe shi da duka saboda dalilai da yawa.

Dalili na farko, za a iya turo matasa haka kawai su yi wa mutum wulakanci. Wannan kuwa aikin abokan takarar ka ne da ka kayar a wurin zabe. Saboda a tunanin su ka dade ka na yi, ka hana wasu ma su hau matsayin na ka. Tunda abu ne kowa so ya ke yi. Sannan kuma akwai talauci ya addabi jama’a da kuma rashin aikin yi da ya yi wa matasa katutu.  To za a iya amfani da marasa aikin yi ana biyan su ‘yan kudi kalilan su aiwatar da wata manufa mummuna ko mai kyau.

Yanzu dai dubi yadda suka fara huce-haushi zan ce ko nuna fushun su a kan shugabannin da suka zaba. To ya zama tilas shugabannin nan su tashi tsaye su shawo kan wannan babbar matsala, tun kafin ta yi munin da za ta annoba, ta yi awon-haba da wanda ya ji ya gani, da wanda bai ji ba bai gani ba.

PT: Wadanne matakai ya kamata a dauka?

IDA: Su dai masu zabe tashin farko su san irin mutanen da za au rika zabe don su wakilce su. Ni dai ban ga fa’idar sayen babura ka raba wa mutum 250 daga cikin milyoyin mutanen da ka ke wakilta ba. Wannan misali ne na bayar. Domin idan ka yi haka, to matsalar mutum 250 kadai ka warware kenan. Ba za ka taba zama wakilin nagari ba har sai ka tashi a cikin majalisa ka kawo kudirin da kawo wa kasar ka ci gaba, sannan kuma ka kawo ayyukan taya kasa a yankin da ka ke wakilta. Ka zama kai ne sanadiyyar Gina musu makaranta, asibiti, madatsun ruwa da sauran su.

Amma magana ta gaskiya fa tilas sai ‘yan siyasa sun canja yanayin takun dangantakar su da talakawa.  Idan ba haka ba kuwa, to an kusa zuwa lokacin da dan siyasa bai iya tashi daga nan ya je can ba tare da an masa kofar-raggo an buge shi ba.

PT: Kai da tsohon gwamnan babban bankin tarayya duk kun rike mukamin Danmaje. Kai ka na Danmajen Katsina, shi ya na Danmajen Kano. To ga shi yanzu shi ne Sarkin Kano, kuma abokin ka ne.  Tunda har yau ka na rike da wannan sarauta, shin ka na ganin kalaman da ke fitowa daga bakin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a kan hanya su ke?

IDA: Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II a da aboki na ne, amma kafin ya zama Sarki. To ka san Hausawa sun ce kowa ya yi Sarki to ya zarce abokan sa. Amma har yanzu muna da kusanci da juna sosai. Mutum ne mai ilmi, mai hangen nesa, mai zurfin tunani, mai kaifin  kwakwalwa, kuma mai son kawo kyakkayawan sauyi ga al’umma.

Ya kamata mu yi la’akari da cewa duk wanda ya yi wani yinkurin kawo wani Sauyi, to za ka ga daga cikin mutanen sa ake fara tsangwamar sa. Haka ta faru ga Annabi Muhammadu (SAW) da wasu Annabawa da yawa da mutanen da suka yi hobbasa wajen karkato al’umma daga wani tsohon tunanin da suke a kai.

Yadda matsaloli suka yi mana yawa a Arewa, kada mu yi tsammani mutum mai ilmi da tunani da hangen nesa kamar Sarkin Kano zai yi zaune wuri daya ya sa amawali ya rufe bakin sa ya na gani matsalolin na cinmu ba tare da ya yi magana ko ya yi wani hobbasa ba. Fata na sauran Sarakuna irin sa su fito su yi koyi da shi. Ya cigaba da magana a kan abin da ya dabaibaye mu a yau da matsalar da ke can gaba ta na jiran mu kasara ta danne mu.

Share.

game da Author