• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Kotu ta yi wa gwamnatin Gombe da ‘yan sanda katanga da dan jarida, Dahiru Kera

    Kotu ta yi wa gwamnatin Gombe da ‘yan sanda katanga da dan jarida, Dahiru Kera

    Samuel Ortom

    Gwamna Ortom ya janye ƙarar da ya maka hadimin sa, wanda ya kayar da shi a zaɓen Sanatan Benuwai, kuma ya roƙi yafiya

    An kara wa ma’aikatan jinya na jihar Yobe albashi

    Akalla mutum 7,806 suka kamu da cutar tarin fuka a tsakanin shekarar 2021 – 2022 a jihar Bauchi

    Iyorchia Ayu ba alheri ba ne, baƙin jinin sa ne ya janyo faɗuwar PDP zaɓen 2023 – Chimaroke Nnamani

    Iyorchia Ayu ba alheri ba ne, baƙin jinin sa ne ya janyo faɗuwar PDP zaɓen 2023 – Chimaroke Nnamani

    Janar Diya, tsohon Mataimakin Janar Abacha ya rasu

    Janar Diya, tsohon Mataimakin Janar Abacha ya rasu

    Kashim Shettima of Borno

    SHARI’AR ZARGIN SHETTIMA YA FITO TAKARA WURI BIYU: Kotu ta kori ƙarar da PDP ta nemi a soke takarar Tinubu da Shettima

    ZAƁEN KANO: Ganduje, Gawuna Garo da APC sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓe, sun yi zanga-zanga a Kano

    ZAƁEN KANO: Ganduje, Gawuna Garo da APC sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓe, sun yi zanga-zanga a Kano

    Ba ayi zabe a Katsina ba, coge aka yi kuma za mu garzaya Kotu – Lado-Danmarke

    Ba ayi zabe a Katsina ba, coge aka yi kuma za mu garzaya Kotu – Lado-Danmarke

    Hyacinth Alia na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Benuwai

    Hyacinth Alia na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Benuwai

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

No Result
View All Result

TATTAUNAWA: Nasarori da Kalubalen Bankin Jaiz a Najeriya – MD Hassan

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
April 11, 2017
in Rahotanni
0
TATTAUNAWA:  Nasarori da Kalubalen Bankin Jaiz a Najeriya – MD Hassan

Duk da rikicin da ya dabaibaye bankin Jaiz a nan Nijeriya tun kafin farkon kafa shi, Manajan Darakta kuma Shugaban Bankin, Hassan Usman ya ce an samu gagarimar nasara a cikin kankanin lokacin fara aikin bakin zuwa yanzu. Wanda hakan ya ba masu zuba jari karfin guiwar yin amanna da cewa bankin ya zauna a Najeriya da kafafun sa.

Ga tattaunawar da shugaban bankin Hassan Usman ya yi da gidan Jaridar Premium Times.

PT: An kafa Bankin Jaiz a shekarun baya ba da dadewa ba, inda ya shigo da wani sabon tsarin banki a Najeriya. Shin ya ake aiwatar da wannan tsari ne zuwa yau?

USMAN: To zan iya cewa kwalliya na ta biyan kudin sabulu. Idan za ka iya tunawa mun fara ne da hannayen jarin da ba su wuce na naira bilyan biyar ba a cikin 2012. Amma a yau muna da masu hannayen jari a cikin bankin daga ko’ina cikn fadin kasar nan, kuma daga kowane bangaren mabiya addini. A lokacin da muka fara sayar da hannayen jari, cikin 2003, mun samu sama da masu hannayen jari dubu ashirin. Daga naira bilyan biyar da muke da ita cikin 2012, a yau mu na da hannun jarin da ya kai naira bilyan 15.

Da farko dai ya kamata a san cewa mun fara ne da rassa guda uku kadai a cikin 2012. Amma a yau mu na da rassa har guda 30. Mun fara tare da kwastoma guda daya tal. Amma a yau mu na da kwastomomi sama da dubu 100.

A cikin shekarar da mu ka fara, an zuba kudade a asusun ajiya da ba su kai naira bilyan 3.5 ba. Amma ya zuwa yau, an zuba kudade a asusun ajiya da suka haura naira bilyan 60. Ba mu samun gibi a duk kididdigar riba da faduwa a karshen shekara. Muna samun tagomashi na kimanin kashi 30 bisa 100 tun daga 2012. Mun kuma yi amanna da cewa wannan tsari ya zama mai dorewa sosai. A matsayin sa na sabon tsarin hada-hadar kudade, mu na ci gaba da samun yarda da amincewa daga dimbin jama’a. A fili ya ke cewa wannan tsari ya zauna daram da gindin sa kenan.

Mun fara a matsayin banki na wata shiyya daya a kasar nan. A yau kuwa muna da rassa a dukkan fadin kasar nan, har da Kudu-maso-Yamma da Kudu-maso-Kudu, sannan kuma za mu ci gaba da bude rassa a sauran yankunan da ke nesa da mu.
A takaice dai, ina jin cewa duk da akwai kalubalen da har yanzu mu ke fuskanta, kamar kowane sauran bankuna, to duk da haka mu na samun kwakkwaran ci gaba mai dorewa a wannan tsarin banki da mu ka shigo da shi. Sannan kuma hakan wani tabbaci ne na samun nasarar kafa wani tsarin banki wanda ake tafiyar da shi a sauran kasashen duniya, wato bankin da babu kudin ruwa.

PT: Ya ku ka wanye da tsoron cewa da farko an rika cewa an kafa bankin ne da nufin cimma wata manufar boye ta addini?

USMAN: A’a, ai wannan mummunar fahimta ce aka yi wa bankin Jaiz. Mu fa wata sabuwar fuska ce ta wani sabon tsarin banki. Babba kuma muhimmin bayanain da mu ke ci gaba da yadawa shi ne wannan banki ba shi da alaka da biyan bukatar wani addini. Komai a bayyane ake yin sa, ido na ganin ido, kowane addini mutum ya ke, ba a boye masa komai. Kawai sabon tsarin hada-hadar kudade ne wanda kai tsaye ya ke gudanar ayyukan da al’umma ke bukata wanda zai fi amfanar su kai tsaye, a karkashin tsarin biyan kudi da ya sha bamban da sauran bankuna.

Kai tsaye irin wannan ayyukan ne wannan banki da babu kudin ruwa ko mu ce Bankin Musulunci ya ke yi a ko’ina cikin duniya. Ya na samar da kudade ne ga jama’ar da ba su iya biyan wasu ayyuka da su ke son aiwatarwa da kudaden su.

To maimakon mu ba mutum kudi, sai mu je mu aiwatar masa da wannan ayyuka ko sayo masa kayayyakin da ya ke bukata din domin amfanin sa ko hada-hadar kasuwancin sa. Daga farawar mu mun sha cin karo da mutane masu halayya iri daban-daban wadanda suka rika zuwa mu na yin huldar kasuwanci da su. To wadannan shi ne irin ayyukan da mu ke yi.

PT: Mun samu labarin an shigar da Bankin Jaiz a cikin bankunan da ke Kasuwar Hada-hadar Hannayen Jari. Shin me ku ke son ku amfana a wannan tsari?

USMAN: Ai na fada tun farko cewa a cikin 2003 ne muka saka hannayen jarinmu a kasuwa. Ko ta wane ma’auni ko matsayi, zan iya cewa mu na samun nasara sosai. Sannan masu kula da hannayen jari sun ba mu damar sakin hannayen jarin mu a kasuwa ga duk mai so ya saya, duk kuwa da cewa mu sabbin-shiga kasuwa ne. Daga cikin alkawurran da muka daukar musu, akwai cewa a cikin shekara uku ko hudu ko biyar, to za mu samu shiga cikin Kasuwar Hada-hadar hannayen jari, wato Stock Exchange.

To kun ga a yau mu na da masu hannayen jari sama da dubu 20. Yawancin wadannan masu hannayen jari, duk masu kananan hannayen jari ne da muka fara da su sama da shekara goma. Shi ya sa mu ka rika su, domin akidar mu ta cika wa abokan hulda alkawari. Sannan abu na biyu kuma, mu na shige masu gaba wajen samar musu yanayin da suke bukatar karfafa hannayen jarin su.

Baya ga wannan kuma, an kara mana kwarin guiwa shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari, domin muna son bankin ya kasance tun farkon kafa shi ya samu dafa’in bin ka’idoji da da’ar da ake bukata kowane bankin ya kasance ya na da ita, sannan kuma mu kara samun nasibin gudanar da komai a sarari, ba nuku-nuku.

Kun ga hakan zai kara kai bankin mu ga jama’a, tare da tabbatar da cewa ko ma wane ne a duniyar nan, zai iya samun sayen hannayen jarinmu. Kuma hakan ne zai sa kowa a duniyar nan zai dauke mu da muhimmanci, zai san lallai ba da wasa mu ke harkar nan ba.

PT: Amma ba a cewa ba ku fama da matsaloli. Idan akwai su, to wadanne matsaloli ku ke fama da su?

USMAN: Matsalar farko ita ce kalubalen da mu ka fuskanta kafin kafa wannan banki, kuma su na da yawa. Amma babbar matsala ita ce rashin wayar wa mutane kai, ba ma ta bangaren su kan su jama’a ba, har ma da bangaren masu sayen hannayen jari a bankin, mahukuntan tsarin bankuna, masu zuba jari, kwastomomi da sauran jama’a baki daya.

Abin farin ciki kuma shi ne, yanzu dai mun shawo wannan matsala ta wayar wa jama’a kai. Yanzu jama’a tuni sun gane cewa Bankin Musulunci ba bankin farfagandar addini ba ne, kawai banki ne da ya shigo da sabon tsarin hada-hadar kasuwanci ta daban da ba a sani ba da farko, domin kara fadada hulda da jama’a da daman gaske.

Sai dai kuma har yanzu akwai sauran ’yan matsaloli dangane da irin huldar da za mu yi da kwastoma. Hatta su kan su wasu masu karajin son a aiwatar da tsarin da babu ruwa din nan, ba su ma san cikakkar ma’anar tsarin ba.

Wasu da dama fa sun dauka kawai aiki ne ne na tallafi, ko agaji ko fisibi Lillahi. Ba su san bambancin tsarin bankin da sauran bankuna ba. Sai idan sun ji labarin cewa za su biya wasu kudaden ladar wata hada-hada da aka yi da su, sannan za su fara wani tunani kuma, har suna mamaki. To idan kwastoma ba zai rika biyan ladar wasu ayyuka da aka yi masa ba, ta ya za a yi kuma banki ya dore kenan?

Kun ga akwai jan aiki a gaban mu a ko yaushe wajen wayar da kan jama’a dangane da tsarin bankinmu. Gaskiyar magana ita ce an kafa bankin Musulunci ce domin a samu riba, ya rike kansa da kansa, sannan su taimaka wa masu hulda da su su samu riba yadda za su kara daratta kasuwanci ko jarin su.

Wani kalubale da mu ka fuskanta kuma shi ne wayar wa masu sa-ido da kula da tsarin bankuna da hada-hadar hannayen jari. Wannan ma zan iya cewa kusan an magance ta. Amma akwai sauran ’yan matsaloli da mu ke kwana mu ke tashi a cikin su.

Sauran kalubalen da mu ke fuskanta kasancewa ba mu dade da shigo da wannan tsarin ba, sun hada da rashin kwararrun ma’aikata masu kyakkyawan horon aiki. Wannan ma babban kalubale ne.

Amma abin lura, babu wani banki da ke cibiyar hada-hadar kudin da ba ta da na ta kalubale. Sai dai mu ce ta mu matsalar kawai muka sani. Duk da hakan kuwa sai kara samun masu hulda da my mu ke yi. Shawo kan matsalolin mutum kuwa shi ne samun nasarar sa.

PT: Sauran bankuna na fama da matsalar musayar kudaden kasashen waje. To ku ma ya ku ke fama da wannan matsalar?

USMAN: To ai wannan matsala ruwan dare ce, ta game duniya. Musayar kudi na da muhimmanci a gare mu, domin mu sayar mu samu riba, sai kuma domin biyan bukatun kwastomomin mu masu bukata domin biyan kudin makarantar yaran su, fita waje duba lafiyar su, ko kuma tafiya hutu. Akwai kuma masu masana’antu da ke son kudaden domin sayo injuna da na’urori.

To matsalar na shafar kwastomomin mu. Idan ka nemi musayar kudi a bankin da ka ke hulda da shi, sai ba ka samu da wuri ba, to kimar bankin zai ragu a idon su. Don haka wannan matsalar ta shafe mu, musamman a cikin 2016.

Ba na fata kuma ina addu’a kada Allah ya maimaita mana irin yadda 2016 ta kasance. Kun ga a wannan shekarar Babban Bankin Nijeriya ya fara magance matsalar wajen sayar wa bankuna kudaden kasashen waje.

To mu kuma ba mu da wani fargaba a kan matsalar Dalar Amurka, domin ba mu karbar ramce ko lamunin Dala daga ko’ina kamar yadda sauran bankuna ke yi.

PT: Ya ku ke ciki da tsarin Sukuk da ku ke son fara aiwatarwa ne?

USMAN: Tarihin Sukuk a Nijeriya ya samo asali ne tun cikin 2014, lokacin da jihar Oshun ta fara yi. To amma tsarin bai ja hankalin mutane ba. Amma dai har yanzu ta na yi, kuma ana samun nasara. Sai dai bai samu karbuwa sosai ba.

A yanzu idan mutum na son sayen tsarin Sukuk na naira milyan 100, zai yi wahala ya samu. Saboda abin da ake samu a sama ya na da daraja sosai. Kowa na saye ne saboda abin da ake samu a sama. Kuma ana biya din duk kuwa da irin matsin tattalin arziki da aka fama da shi.

Tsarin Sukuk ya na da kyau sosai, domin bai yiwuwa mutum ya karba ya karya ka’ida. To tsarin Sukuk na gaba da muke jira, shi na game-gari ne.

Babban Bankin Nijeriya, CBN ne ke samar da wadatar tsarin yadda za a zuba jari, tunda kudi na ga CBN din. Wannan kuma nauyi ne na Ma’aikatar kudi ta Tarayya tare da hadin guiwar Ofishin Kula da Basussuka. To mu kuma a halin yanzu tuni mun rigaya mun cika sharuddan su, har sun aminta da mu.

Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ta yi mana alkawarin farawa da mu a cikin farkon watannin nan hudu na wannan shekara da muke ciki. To amma kun san irin wannan da wahala a sa rana ba a daga ba.

Kun san kuma sai an samo aikin da za a yi da kudin. Kuma na tabbata kun dai san shi tsarin Sukuk ba kai tsaye za a dauki makudan kudade a ba ka ba, sai an samu abin da aka rike a hannu na kadarorin ka tukunna.

Mun sha cewa jami’an gwamnati tsarin Sukuk fa ya fi tasiri, domin bai yiwuwa mutum ya kasa bilyan kudin da ya karba ko ya karkatar da kudin. Saboda ana sa-ido, ana kula kuma ana taka-tsantsan.

A tsarin Sukuk ana tabbatar da cewa an yi dukkan abin da aka karbi kudin domin yin sa. Kuma zai kasance ayyuka ko kwangiloli ne aka yi wadanda idanu za su iya gani kuru-kuru.

To muna fatan Mai’aikatar Kudi ta Tarayya da Ofishin Kula da Hada-hadar Basussuka za su gaggauta samar mana da wannan tsarin nan da wasu ‘yan watanni masu zuwa.

Shi tsarin Sukuk ya bambanta da sauran tsarin karbar kudi, ya fi karbar bashi garanti wajen yin hulda. Ya kamata a fadada tsarin Sukuk domin mu samu kwararowar masu Zuba jari daga kasashen Gabas ta Tsakiya da sauran kasashen da ke shakkun zuwa su juba jari a Nijeriya.

PT: Ka ce ba ka fatan a maimaita irin matsalar 2016. To wane irin hasashe ka ke yi wa 2017?

USMAN: Ina ganin 2017 ai ta fara nuna alamun za ta fi 2016 nesa ba kusa ba. Matsawar Babban Bankin Nijeriya, CBN ya ci gaba da wadatar wa bankuna kudaden musaya na kasashen waje.

Sannan kuma idan gwamnatin tarayya ta ci gaba da kashe kudade wajen farfado da tattalin arziki, kuma idan aka cin gaba da inganta fannin makamashi da lantarki.

Haka kuma idan farashin danyen mai a duniya ya kara tashi, daga Dala 50 kowace gangar mai, to na yi amanna 2017 za ta yi albarka sosai kuma za ta inganta tattalin arziki.

Karanta tattaunawar a shafin mu na Turanci a nan: INTERVIEW: The successes, challenges of Jaiz Bank in Nigeria – MD Hassan Usman

Tags: AbujaBankiHausaIslamJaiz BankLabaraiNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

Alluran Rigakafin Sankarau kyauta ne – Gwamnati

Next Post

Tonon Silili: EFCC ta kama naira miliyan 250 a kasuwan ‘yan canji

Next Post
Tonon Silili: EFCC ta kama naira miliyan 250 a kasuwan ‘yan canji

Tonon Silili: EFCC ta kama naira miliyan 250 a kasuwan 'yan canji

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Bashin da ake bin Najeriya ya mirgina cikin ramin naira tiriliyan 46.25 kafin shiga 2023 – DMO
  • Kotu ta daure Surajo Hamza da ya yi lalata da matan aure da karfin tsiya a Abuja
  • ANA WATA GA WATA: Rundunar SSS ta bankado ‘makircin’ wasu gwaskwayen Najeriya da ke kitsa yadda za a ruguza mika mulki ga ‘Tinubu’ a kafa gwamnatin rikon kwarya
  • Kotu ta yi wa gwamnatin Gombe da ‘yan sanda katanga da dan jarida, Dahiru Kera
  • ZAƁEN GWAMNAN KANO: Gawuna, ɗan takarar APC ya rungumi ƙaddara, ya taya Abba Gida-gida na NNPP murna

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Labarai
  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.