Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin shugabannin hukumomi da ma’aikatun da ke karkashin ma’akatar Ilimi 19.
Babban darektan watsa labaran ma’aikatan Ilimin Chinenye Ihuoma ne ta sanar da hakan wa kamfanin dillancin Labarai.
Ihuoma tace Buhari ya duba cancanta da kwarewa kafin nada wadanda aka tabbatar wa kujerun ma’aikatun.
Wadanda aka nada sun hada da
Ayo Banjo, Hukumar Kula da jami’o’I na Kasa
Emeka Nwajiuba, Asusun bada tallafi ga Jami’o’i
Ekaete Okon, Hukumar tsarawa da gudanar da ilimi ta kasa, NIEPA.
Mahmud Mohammed, Tsarin bada ilmi na bai daya, UBEC
Zainab Alkali, Hukumar kula da dakunan karatu ta Kasa.
Abubakar Saddiq, Hukumar Shirya Jarabawa ta NECO
Gidado Akko, Hukumar wayar da kan mutane da samar da Ilimin yaki da jahilci na kasa, NMEC.
Gidado Tahir, Hukumar samar da ilimi ga makiyaya, NCNE
Leonard Karshima, Hukumar kula da ilimin kasuwanci, kimiya da fasaha ta kasa, NABTEB
Adamu Baikie, Cibiyar yiwa malamai rajista ta kasa,TRCN
Maigari Dingyadi, Hukumar kula da kwalejojin ilimi na kasa, NCCE
Kaka Yale, Hukumar Koyar da Malamai, NTI
Buba Bajoga, Cibiyar Kula da al’amurran lissafi ta kasa NMC
Emmanuel Ndukwe, Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i JAMB
N. N. Nnabuchi, Cibiyar bunkasa harsuna ta kasa, NINLAN.
Paul Unongo, Hukumar bincike da bunkasa ilimi ta kasa,
NERDC
Saliba Mukoro, Hukumar bunkasa harshen faransanci ta kasa, NFLV
Modupe Adelabu, Hukumar kula da ilimin kimiya da fasaha ta kasa.