Shugaban jam’iyyar APC da wadansu ‘ya’yan jam’iyyar sama da 800 ne suka canza sheka zuwa jam’iyyar PDP a karamar hukumar Nsit Ubium, dake jihar Akwa-Ibom.
Da ya ke jagorantar dandazon ‘yan jam’iyyar shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Nsit din Aniefiok Ekahya ce yunwa da talauci ne ya sa su duka suka gudu daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.
“Ga takardu da shaidojin shigan mu jam’iyyar APC duk ku kona domin yanzu ba mu yinta kaf din mu.
Shugaban jam’iyyar PDP a jihar ya yi maraba da shigowa jam’iyyar sannna yace ba za su nuna musu bambamci ba.