A yau ne mai shari’a Binta Nyako ta bada belin dan yakin neman kafa jamhuriyar Biafra, Nnamdi Kanu.
Ga Sharuddan belin da kotu ta gindaya masa
1 – Kada ya sake ya tsaya ko ya zauna tare da gungun mutanen da suka haura 10.
2 – Kada ya sake ya yi hira da ‘yan jarida.
3 – Kada ya tara gangamin jama’a.
4 – Ba za a karbi belin saba, har sai ya kawo mutane uku sun tsaya masa tare da ajiye kudi naira milyan 100 kowanensu.
5 – Daya daga cikin masu karbar belin ya kasance wani babban mutum ne kuma Inyamiri, kamar ko Sanata ko makamancin hakan.
6 – Mai karbar belin na biyu ya kasance Bayahude ne, tunda Nnamdi Kanu adddinin Yahudawa ya ke bi.
7 – Mai karbar beli na uku ya kasance babban mutum ne mazaunin Abuja, wanda ya mallaki gida ko fili a Abuja.
8 – Tilas Nnamdi Kanu ya bai wa kotu ajiyar Pasport din sa na fita kasasshen waje.
9 – Shi ma passport din sa na kasar Birtaniya ana so ya bayar wa kotun ajiyar sa.
10 – Ana so duk wata ya kai wa kotu bayanin irin saukin da ya ke samu da kuma irin kulawar da likitoci suka yi masa.