Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya yi kira ga mutanen Najeriya da su guji shan magani ba tare da samun tabbacin haka ba daga kwararrun likitoci saboda a iya kawo karshen annobar sankarau.
Sarkin ya fadin hakan ne a wata takarda da ya saka ma hannu wanda mai martaba sarkin Argungu Samaila Mera ya sanar wa kamfanin dillancin labarai.
Sarkin Argungu yace Sarkin Musulmin ya yi kira ga iyaye da ma’aikatan kiwon lafiya su wayar da kan mutane wajen sanar dasu amfanin bude tagogi a dakuna da duk inda suke kwana sannan kuma a rage yin cinkos a wuri daya.
Ya kuma kara da cewa duk wanda aka ga alamar ya kamu da cutar ya yi kokarin zuwa asibiti da ke kusa da shi domin samun magani.
Sarkin Musulmi ya bada shawara da a gudanar da wani babban taro na gaggawa da zai hada da sarakunan arewa da malaman asibiti domin ganin a kawo karshen wannan annoba da ta addabi mutanen yankin.
Shugaban kula da cututtuka na Najeriya NCDC Lawal Bakare ya sanar da cewa a yanzu haka mutane 336 ne suka rasa rayukansu sanadiyar bullowar cutar.
Bakare ya ce hukumar NCDC za ta yi aiki tukuru da neman hadin guiwar masana musamman a fannin kiwon lafiya domin samar da cibiyoyin kiwon lafiya da za su ba da kula na gaggawa ga mutanen da ke dauke da cutar domin rage yaduwar ta.
Ya kuma kara da cewa kasa Najeriya na da alluran rigakafin cutar sankarau da ya kai 500,000 kuma za’a raba su ne ga jihohin da suke bukata.
Ya ce za su samu karin tallafin alluran rgakafin daya kai 823,970 daga kasar Britaniya.